Luka 18:14-19
14
“Ina gaya muku, wannan mutum ne, ba ɗayan ba, ya koma gida baratacce, babu laifi a gaban Allah. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”
15
Mutane suna kawo jarirai wurin Yesu don yă taɓa su. Da almajiransa suka ga haka, sai suka kwaɓe su.
16
Amma Yesu ya kira yaran a wurinsa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina. Kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne.
17
Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ba zai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.”
18
Wani mai mulki ya tambayi Yesu ya ce, “Malam managarci, me zan yi don in gāji rai madawwami?”
19
Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake kira na managarci? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai.
Settings