Skip to content
Luka 14:1-16

Luka 14:1-16

1
Wata ranar Asabbaci, da Yesu ya shiga gidan wani sanannen Bafarisiye don cin abinci, sai mutane suka zuba masa ido da kyau.
2
A nan a gabansa kuwa akwai wani mutum mai ciwon kumburin ƙafa da hannu.
3
Sai Yesu ya tambayi masanan dokoki da Farisiyawa ya ce, “Daidai ne bisa ga doka, a yi warkarwa a ranar Asabbaci, ko babu?”
4
Amma ba su ce kome ba. Sai ya riƙe mutumin, ya warkar da shi, sa’an nan ya sallame shi.
5
Sai ya tambaye, su ya ce, “In wani a cikinku yana da ɗa, ko bijimi da ya faɗa a rijiya a ranar Asabbaci, ba za ku cire shi nan da nan ba?”
6
Suka rasa abin faɗi.
7
Da ya lura da yadda baƙi suna zaɓan wuraren zama masu bangirma a tebur, sai ya faɗa musu wannan misali, ya ce;
8
“In wani ya gayyace ka bikin aure, kada ka zaɓi wurin zama mai bangirma, don wataƙila akwai wani da ya fi ka girma, da aka gayyata.
9
In kuwa haka ne, wanda ya gayyace duk biyunku, zai zo ya ce maka, ‘Ka ba wa mutumin nan wurin zamanka.’ Ka ga, an ƙasƙantar da kai, kuma dole ka ɗauki wuri mafi ƙasƙanci.
10
Amma in an gayyace ka, ɗauki wuri mafi ƙasƙanci, don in wanda ya gayyace ka ya zo, zai ce maka, ‘Ka hawo nan aboki a wuri mafi girma.’ Wannan zai ɗaukaka ka a gaban dukan ’yan’uwanka baƙi.
11
Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Shi wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”
12
Sai Yesu ya ce wa wanda ya gayyace shi, “Lokacin da ka shirya biki ko liyafa, kada ka gayyaci abokanka, ko ’yan’uwanka, ko danginka, ko kuma maƙwabtanka masu arziki, gama in ka yi haka, suna iya gayyatarka, su biya maka alherin da ka yi musu.
13
Amma lokacin da ka kira biki, ka gayyaci matalauta, da guragu, da shanyayyu, da makafi.
14
Ta haka, za ka sami albarka. Ko da yake ba za su iya biyan ka ba, za a biya ka a ranar tashin masu adalci daga matattu.”
15
Da jin haka, sai wani da yake tare da shi a tebur ɗin, ya ce wa Yesu, “Mai albarka ne wanda zai ci abinci a bikin nan a mulkin Allah.”
16
Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum yana shirya wani babban biki, ya kuma gayyaci baƙi da yawa.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options