Luka 12:54-59
54
Ya ce wa taron, “Sa’ad da kuka ga hadari ya fito daga yamma, nan da nan kukan ce, ‘Za a yi ruwan sama,’ sai a kuwa yi.
55
Sa’ad da kuma iska ta taso daga kudu, kukan ce, ‘Za a yi zafi,’ sai kuwa a yi.
56
Munafukai! Kuna san yadda za ku fassara yanayin ƙasa da na sararin sama. Ta yaya ba ku san yadda za ku yi fassarar wannan zamani ba?
57
“Don me ba ku iya auna wa kanku, abin da yake daidai ba?
58
Yayinda kake kan hanyar zuwa kotu da maƙiyinka, ka yi matuƙar ƙoƙari ku shirya tun kuna kan hanya. In ba haka ba, zai kai ka gaban alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga ɗan sanda, ɗan sanda kuma ya jefa ka a kurkuku.
59
Ina gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.”
Settings