Tsallake zuwa abun ciki
Firistoci 18:6-18

Haramtattun Hulɗar Jima’i

Firistoci 18:6-18
6
“ ‘Kada wani ya kusaci wani dangi na kusa don yă yi jima’i. Ni ne Ubangiji.
7
“ ‘Kada ka ƙasƙantar da mahaifinka ta wurin kwana da mahaifiyarka. Ita mahaifiyarka ce; kada ka yi jima’i da ita.
8
“ ‘Kada ka yi jima’i da matar mahaifinka, wannan zai ƙasƙantar da mahaifinka.
9
“ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwarka, ko ’yar mahaifinka ko ’yar mahaifiyarka, ko an haife ta a gida ɗaya da kai ko kuwa a wani wuri dabam.
10
“ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar ɗanka ko ’yar ’yarka, wannan zai ƙasƙantar da kai.
11
“ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar matar mahaifinka wadda aka haifa wa mahaifinka; ita ’yar’uwarka ce.
12
“ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwar mahaifinka, ita dangin mahaifinka ne na kusa.
13
“ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwar mahaifiyarka, domin ita dangin mahaifiyarka ce na kusa.
14
“ ‘Kada ka ƙasƙantar da ɗan’uwan mahaifinka ta wurin kusaci matarsa don ka yi jima’i da ita, ita bābarka ce.
15
“ ‘Kada ka yi jima’i da matar ɗanka. Ita matar ɗanka ne; kada ka yi jima’i da ita.
16
“ ‘Kada ka yi jima’i da matar ɗan’uwanka; wannan zai ƙasƙanta ɗan’uwanka.
17
“ ‘Kada ka yi jima’i da mace da kuma ’yarta. Kada ka yi jima’i da ’yar ɗanta ko ’yar ’yarta; su danginta ne na kusa. Wannan mugun abu ne.
18
“ ‘Kada ka auri ’yar’uwar matarka ta zama kishiyar matarka ka kuma yi jima’i da ita yayinda matarka tana da rai.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options