Firistoci 18:19-23
19
“ ‘Kada ka kusaci mace don ka yi jima’i da ita a lokacin ƙazantar al’adarta.
20
“ ‘Kada ka yi jima’i da matar maƙwabcinka ka ƙazantar da kanka tare da ita.
21
“ ‘Kada ku ba da wani daga cikin ’ya’yanku don a yi hadaya wa Molek, gama ba za ku ƙasƙantar da sunan Allahnku ba. Ni ne Ubangiji.
22
“ ‘Kada ka kwana da namiji kamar yadda namiji yakan kwana da ta mace, wannan abin ƙyama ne.
23
“ ‘Kada ka yi jima’i da dabba ka ƙazantar da kanka. Mace ba za tă ba da kanta ga dabba don yă yi jima’i da ita ba; wannan abin ƙyama ne.
Settings