Skip to content
Firistoci 15:1-18

Firistoci 15:1-18

1
Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
2
“Yi wa Isra’ilawa magana, ku ce musu, ‘Duk sa’ad da wani namiji yake ɗiga daga azzakarinsa, wannan ɗiga marar tsarki ne.
3
Ko ɗigar ta ci gaba da fitowa daga azzakarinsa ko an tsere ta, za tă sa mutumin yă zama marar tsarki. Ga yadda ɗigarsa za tă kawo ƙazantuwa,
4
“ ‘Duk gadon da mutumin mai ɗigar ya kwanta a kai, zai zama marar tsarki, kuma duk abin da ya zauna a kai, zai zama marar tsarki.
5
Duk wanda ya taɓa gadonsa dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma.
6
Duk wanda ya zauna a inda wannan mai ɗiga ya zauna a kai, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma.
7
“ ‘Duk wanda ya taɓa jikin mai ɗiga, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
8
“ ‘In mai ɗiga ya tofa miyau a kan wani wanda yake tsarkakakke, dole tsarkakakken nan yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
9
“ ‘Kowane sirdi da mai ɗigar ya zauna a kai zai ƙazantu,
10
kuma duk wanda ya taɓa wani abu cikin abubuwan da suke a ƙarƙashin sirdin zai ƙazantu har yamma; duk wanda ya ɗauki abubuwan nan dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma.
11
“ ‘Duk wanda mai ɗiga ya taɓa ba tare da ya wanke hannuwansa da ruwa ba, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
12
“ ‘Dole a farfashe tukunya lakar da mutumin ya taɓa, kuma dole a ɗauraye duk wani abin da aka yi da katako wanda ya taɓa da ruwa.
13
“ ‘Sa’ad da aka tsabtacce mai ɗigar, zai ɗauki kwana bakwai don tsabtaccewarsa; dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka mai tsabta, zai kuwa zama tsarkakakke.
14
A rana ta takwas dole yă ɗauki kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, yă zo gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada, yă ba da su ga firist.
15
Firist ɗin zai miƙa su, ɗaya domin hadaya don zunubi, ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa. Ta haka zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mai ɗigar.
16
“ ‘Sa’ad da namiji ya ɗigar maniyyi, dole yă wanke jikinsa gaba ɗaya da ruwa, zai kuma ƙazantu har yamma.
17
Dole a wanke duk riga ko fatar da yake da maniyyin a kansa da ruwa, zai kuma ƙazantu har yamma.
18
Sa’ad da namiji ya kwana da mace ya kuwa zub da maniyyi, dole dukansu biyu su yi wanka, za su kuma ƙazantu har yamma.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options