Firistoci 15:2-12
2
“Yi wa Isra’ilawa magana, ku ce musu, ‘Duk sa’ad da wani namiji yake ɗiga daga azzakarinsa, wannan ɗiga marar tsarki ne.
3
Ko ɗigar ta ci gaba da fitowa daga azzakarinsa ko an tsere ta, za tă sa mutumin yă zama marar tsarki. Ga yadda ɗigarsa za tă kawo ƙazantuwa,
4
“ ‘Duk gadon da mutumin mai ɗigar ya kwanta a kai, zai zama marar tsarki, kuma duk abin da ya zauna a kai, zai zama marar tsarki.
5
Duk wanda ya taɓa gadonsa dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma.
6
Duk wanda ya zauna a inda wannan mai ɗiga ya zauna a kai, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma.
7
“ ‘Duk wanda ya taɓa jikin mai ɗiga, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
8
“ ‘In mai ɗiga ya tofa miyau a kan wani wanda yake tsarkakakke, dole tsarkakakken nan yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
9
“ ‘Kowane sirdi da mai ɗigar ya zauna a kai zai ƙazantu,
10
kuma duk wanda ya taɓa wani abu cikin abubuwan da suke a ƙarƙashin sirdin zai ƙazantu har yamma; duk wanda ya ɗauki abubuwan nan dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma.
11
“ ‘Duk wanda mai ɗiga ya taɓa ba tare da ya wanke hannuwansa da ruwa ba, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
12
“ ‘Dole a farfashe tukunya lakar da mutumin ya taɓa, kuma dole a ɗauraye duk wani abin da aka yi da katako wanda ya taɓa da ruwa.
Settings