Skip to content
Mahukunta 9:1

Mahukunta 9:1

Ana nuna aya 1 tare da mahallin da ke kewaye.

Abimelek Ya Nemi Sarauta a Shekem

1
Abimelek ɗan Yerub-Ba’al ya tafi Shekem wurin ’yan’uwan mahaifiyarsa, ya ce musu da kuma dukan dangin mahaifiyarsa,
2
“Ku tambayi ’yan ƙasar Shekem, ‘Wanne ya fi muku, a sa dukan ’ya’yan Yerub-Ba’al saba’in maza su yi mulkinku, ko dai mutum guda kawai yă yi mulkinku?’ Ku tuna, ni jininku ne.”
3
Sa’ad da ’yan’uwan suka mayar wa ’yan ƙasar Shekem wannan, sai suka goyi bayan Abimelek, gama sun ce, “Shi ɗan’uwanmu ne.”
4
Suka ba shi shekel saba’in na azurfa daga haikalin Ba’al-Berit, Abimelek kuwa ya yi amfani da shi ya yi hayar ’yan tauri waɗanda suka zama masu binsa.

Nazarin nassin nan

Sharhi a kan nassin, ba aya ɗaya ba

Sauran wuraren da Nassi ya faɗi haka

  • Mahukunta 8:31

    Yana kuma da ƙwarƙwara wadda take Shekem, ita ma ta haifa masa ɗa wanda ya ba shi suna Abimelek.
    daga aya ta 1
  • Zabura 83:2

    Dubi yadda abokan gābanka suke fariya, dubi yadda maƙiyanka suke ɗaga kansu.
    daga aya ta 1
  • Zabura 83:4

    Suna cewa, “Ku zo, bari mu hallaka su ɗungum a matsayin al’umma, don kada a ƙara tuna da sunan Isra’ila.”
    daga aya ta 1
  • 1 Sarakuna 12:1

    Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan Isra’ila sun je can don su naɗa shi sarki.
    daga aya ta 1
  • 1 Sarakuna 12:3

    Saboda haka mutane suka aika Yerobowam yă zo, sai shi da dukan taron Isra’ila suka tafi wurin Rehobowam, suka ce masa,
    daga aya ta 1
  • 1 Sarakuna 12:20

    Sa’ad da dukan Isra’ilawa suka ji Yerobowam ya dawo, sai suka aika, suka kira shi zuwa taro, suka kuma naɗa shi sarki bisa dukan Isra’ila. Kabila Yahuda kaɗai ta kasance mai biyayya ga gidan Dawuda.
    daga aya ta 1
  • 2 Sama’ila 15:6

    Absalom ya yi ta yin haka ga dukan Isra’ilawan da suka zo wurin sarki don neman adalci, ta haka kuwa ya saci zukatan mutanen Isra’ila.
    daga aya ta 1
  • Farawa 33:18

    Bayan Yaƙub ya zo daga Faddan Aram, ya iso lafiya a birnin Shekem a Kan’ana, ya kuma kafa sansani a ƙofar birni.
    daga aya ta 1
  • Farawa 34:2

    Sa’ad da Shekem ɗan Hamor Bahiwiye mai mulkin wurin ya gan ta, sai ya kama ta, ya kwana da ita, ya ɓata ta.
    daga aya ta 1
  • Irmiya 18:18

    Suka ce, “Zo mu shirya wa Irmiya maƙarƙashiya; gama koyarwar doka da firist ya yi ba za tă ɓace ba, haka ma shawara daga mai hikima da kuma magana daga annabawa. Saboda haka ku zo, mu fāɗa masa da harsunanmu kada mu saurari wani abin da zai faɗa.”
    daga aya ta 1
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options