Mahukunta 1:21-36
21
Ko da yake mutanen Benyamin sun kāsa su kori Yebusiyawa, waɗanda suke zaune a Urushalima; har yă zuwa yau, Yebusiyawa suna zaune a can tare da mutanen Benyamin.
22
To, gidan Yusuf suka auka wa Betel, Ubangiji kuwa yana tare da su.
23
Sa’ad da suka aike mutane don su leƙi asirin Betel (da dā ake kira Luz),
24
’yan leƙen asirin suka ga wani ya fito daga birnin sai suka ce masa, “Ka nuna mana yadda za mu shiga birnin, mu kuwa za mu yi maka alheri.”
25
Saboda haka ya nuna musu, suka kuwa hallaka birnin, suka bar mutumin da dukan iyalinsa da rai.
26
Sa’an nan ya tafi ƙasar Hittiyawa, inda ya gina birni ya kuma kira shi Luz, haka ake kira birnin har wa yau.
27
Amma Manasse ba su kori mutane Bet-Sheyan ko Ta’anak ko Dor ko Ibileyam ko Megiddo tare da ƙauyukansu ba, gama Kan’aniyawa sun dāge su zauna a wannan ƙasa.
28
Sa’ad da Isra’ila ta yi ƙarfi, sai suka tilasta Kan’aniyawa yin aikin gandu amma ba su kore su gaba ɗaya ba.
29
Haka Efraim ma bai kori Kan’aniyawa da suke zaune a Gezer ba, amma Kan’aniyawa suka ci gaba da zama tare da su.
30
Haka kuma Zebulun bai kori Kan’aniyawa da suke zaune a Kitron da Nahalol, waɗanda suka rage a cikinsu ba; sai dai sun sa su aikin gandu.
31
Haka Asher ma bai kori waɗanda suke zama a Akko ko Sidon ko Ahlab ko Akzib ko Helba ko Afik ko kuma Rehob ba,
32
kuma saboda wannan ne mutanen Asher suke zaune cikin mazaunan ƙasar Kan’aniyawa.
33
Haka kuma Naftali bai kori waɗanda suke zaune a Bet-Shemesh ko Bet-Anat; amma mutanen Naftali su ma suna zama a ciki Kan’aniyawa mazaunan ƙasar, waɗanda suke zaune a Bet-Shemesh da Bet-Anat kuwa suka zama masu yi musu aikin gandu.
34
Amoriyawa suka matsa wa mutanen Dan a ƙasar tudu, ba su yarda musu su gangaro zuwa filaye ba.
35
Su Amoriyawa kuma suka dāge su zauna a Dutsen-Heres, Aiyalon, da Sha’albim. Amma yayinda mutanen Yusuf suka ƙara ƙarfi, sai suka su yin musu aikin gandu.
36
Iyakar Amoriyawa kuwa daga Mashigin Kunama zuwa Sela da kuma zuwa gaba.
Settings