Skip to content
Yoshuwa 4:17-24

Yoshuwa 4:17-24

17
Sai Yoshuwa ya umarci firistoci ya ce, “Ku fito daga cikin Urdun.”
18
Firistocin kuwa suka fito daga kogin ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji. Nan da nan da ƙafafunsu suka taɓa busasshiyar ƙasa, sai ruwan Urdun ya gangaro ya cika kogin kamar yadda yake a dā.
19
A rana ta goma ga wata na farko, mutane suka haura daga Urdun suka sauka a Gilgal a gabashin iyakar Yeriko.
20
Sai Yoshuwa ya kafa duwatsu goma sha biyun nan da suka ɗauko daga Urdun.
21
Ya ce wa Isra’ilawa, “Nan gaba in yaranku suka tambayi iyayensu suka ce, ‘Mece ce ma’anar waɗannan duwatsun?’
22
Ku ce musu, ‘Isra’ilawa sun ƙetare kogin Urdun a kan busasshiyar ƙasa.’
23
Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruwan Urdun ya yanke a gabanku, har sai da kuka gama wucewa, kamar yadda ya yi a Jan Teku, a lokacin da ya busar da shi a gabanmu har sai da muka gama wucewa.
24
Ya yi wannan ne domin dukan mutanen duniya su san cewa Ubangiji mai iko ne, domin kuma ku zama masu tsoron Ubangiji Allahnku.”

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options