Yoshuwa 4:10-14
10
Firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suka tsaya a tsakiyar Urdun, har aka gama dukan abin da Ubangiji ya umarci Yoshuwa yă gaya wa mutane, kamar yadda Musa ya ce Yoshuwa yă yi. Mutanen suka wuce da sauri.
11
Sai da dukan mutanen suka wuce sa’an nan akwatin alkawari da firistoci suka sha gaba.
12
Mutanen Ruben, Gad da rabin kabilar Manasse suka ƙetare da shirin yaƙi, suka wuce gaban Isra’ila kamar yadda Musa ya ce su yi.
13
Wajen mutum dubu arba’in shirye domin yaƙi, suka wuce a gaban Ubangiji zuwa filayen Yeriko.
14
A ranan nan Ubangiji ya ɗaukaka Yoshuwa a gaban Isra’ilawa; suka kuma ba shi girma dukan kwanakin ransa, kamar yadda suka girmama Musa.
Settings