Yoshuwa 17:5-9
5
Dalilin ke nan Manasse ya sami kashi goma ban da ƙasar Gileyad da Bashan a gabashin Urdun,
6
domin ’ya’ya mata na kabilar Manasse sun sami gādo tare da ’ya’ya maza. Aka ba wa sauran mutanen kabilar Manasse ƙasar Gileyad.
7
Iyakar ƙasar Manasse ta tashi daga Asher zuwa Mikmetat a gabashin Shekem. Iyakar kuma ta miƙe har zuwa kudu wadda ta ƙunshi mutanen da suke zaune a En Taffuwa.
8
(Manasse ne yake da ƙasar Taffuwa, amma garin Taffuwa kansa, a kan iyakar Manasse ta mutanen Efraim ce.)
9
Sa’an nan iyakar ta ci gaba ta yi kudu zuwa Rafin Kana. Akwai garuruwan da suke kudancin rafin, waɗanda suke Efraim, ko da yake suna cikin yankin Manasse. Iyakar Manasse ta miƙe zuwa arewa ta bi gefen rafin ta kuma ƙarasa a Bahar Rum.
Settings