Yoshuwa 10:1-15
1
Adoni-Zedek sarkin Urushalima ya ji cewa Yoshuwa ya ci Ai da yaƙi ya kuma hallaka ta sarai, ya yi wa Ai da sarkinta abin da ya yi wa Yeriko da sarkinta, mutanen Gibeyon kuwa sun yi yarjejjeniya ta salama da Isra’ilawa, suna kuma zama kusa da su.
2
Shi da mutanensa suka ji tsoron wannan sosai, gama Gibeyon muhimmiyar birni ce, har ma kamar ɗaya daga cikin biranen sarauta, ya ma fi Ai girma, mazanta duka kuwa mayaƙa ne na ƙwarai.
3
Saboda haka sai Adoni-Zedek sarkin Urushalima ya roƙi Hoham sarkin Hebron, Firam sarkin Yarmut, Yafiya sarkin Lakish da Debir sarki Eglon ya ce,
4
“Ku zo ku taimake ni in kai wa Gibeyon hari. Domin sun yi yarjejjeniya ta salama da Yoshuwa da Isra’ilawa.”
5
Sai sarakunan nan biyar na Amoriyawa, sarakunan Urushalima, Hebron, Yarmut, Lakish da Eglon suka haɗa sojojinsu. Suka je dukansu suka yi shirin kai wa Gibeyon hari.
6
Sai mutanen Gibeyon suka aika zuwa wurin Yoshuwa a sansani a Gilgal, “Kada ka juya wa bayinka baya, ka zo da sauri ka cece mu! Ka taimake mu domin sarakunan Amoriyawa duka daga kan tudu sun haɗa ƙarfinsu tare za su tasar mana.”
7
Saboda haka Yoshuwa ya tashi da rundunarsa duka, tare da dukan jarumawansa.
8
Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Kada ka ji tsoronsu; na ba ka su a hannunka. Ba waninsu da zai iya tsayayya da kai.”
9
Bayan sun yi tafiya dukan dare daga Gilgal, Yoshuwa ya auko musu ba labari.
10
Ubangiji ya sa suka ruɗe a gaban Isra’ilawa, Isra’ilawa kuwa suka yi babbar nasara a kansu a Gibeyon. Isra’ilawa suka fafare su a kan hanyar zuwa Bet-Horon suka karkashe su duka har zuwa Azeka da Makkeda.
11
Suna guje wa Isra’ilawa suna gangarawa a kan hanyar Bet-Horon har zuwa Azeka, sai Ubangiji ya turo manyan duwatsu daga sararin sama suka karkashe su, waɗanda manyan duwatsun suka kashe sun fi waɗanda Isra’ilawa suka kashe da takobi.
12
A ranar da Ubangiji ya ba da Amoriyawa a hannun Isra’ilawa, Yoshuwa ya ce wa Ubangiji a gaban Isra’ilawa, “Ke rana, ki tsaya cik a Gibeyon Kai wata, ka je Kwarin Aiyalon.”
13
Sai rana ta tsaya cik, wata kuma ya tsaya, har sai da al’ummar ta ɗauki fansa a kan abokan gābanta, kamar yadda aka rubuta a cikin littafin Yashar. Rana ta tsaya a sararin sama, ba tă fāɗi ba har kusan yini guda.
14
Ba a taɓa ganin abu haka ba ko dā can, ranar da Ubangiji ya saurari mutum. Ba shakka Ubangiji yana yaƙi domin Isra’ilawa.
15
Sai Yoshuwa ya koma sansanin Gilgal tare da dukan Isra’ilawa.
Settings