Přejít k obsahu
Yohanna 5:10-18

Yohanna 5:10-18

10
saboda haka kuwa Yahudawa suka ce wa mutumin da aka warkar, “Yau Asabbaci ne; doka ta hana ka ɗauki tabarmarka.”
11
Amma ya amsa ya ce, “Mutumin da ya warkar da ni shi ya ce mini, ‘Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.’ ”
12
Sai suka tambaye shi suka ce, “Wane ne wannan da ya ce maka ka ɗauke ta ka yi tafiya?”
13
Mutumin da aka warkar kuwa bai ma san ko wane ne ba ne, gama Yesu ya ɓace cikin taron da yake can.
14
Daga baya Yesu ya same shi a haikali ya ce masa, “Ga shi, ka warke. Ka daina yin zunubi, in ba haka ba wani abin da ya fi wannan muni zai iya samunka.”
15
Sai mutumin ya je ya gaya wa Yahudawa cewa Yesu ne ya warkar da shi.
16
To, domin Yesu yana yin waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci, sai Yahudawa suka tsananta masa.
17
Yesu ya ce musu, “Ubana yana cikin aikinsa kullum har yă zuwa wannan rana, haka ni ma, ina kan aiki.”
18
Don haka Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi; ba don yă karya Asabbaci kawai ba, har ma yana ce Allah Ubansa ne, yana mai da kansa daidai da Allah.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options