Yohanna 14:15-21
15
“In kuna ƙaunata za ku yi biyayya da umarnina.
16
Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada,
17
Ruhun gaskiya. Duniya ba ta iya karɓarsa, don ba ta ganinsa ba ta kuma san shi ba. Amma kun san shi, saboda yana zama tare da ku zai kuma kasance a cikinku.
18
Ba zan bar ku marayu ba; zan zo wurinku.
19
Ba da daɗewa ba, duniya ba za tă ƙara ganina ba, amma za ku gan ni. Don ina raye, ku ma za ku rayu.
20
A ranan nan za ku sani ina cikin Uba, ku kuma kuna cikina, ni kuma ina cikinku.
21
Duk wanda yake da umarnaina yana kuma yin biyayya da su, shi ne wanda yake ƙaunata. Wanda yake ƙaunata kuwa Ubana zai ƙaunace shi, ni ma zan ƙaunace shi, in kuma bayyana kaina gare shi.”
Settings