Yohanna 10:11-28
11
“Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin.
12
Wanda aka ɗauko haya ba shi ne makiyayi mai tumakin ba. Saboda haka sa’ad da ya ga kyarkeci yana zuwa, sai yă sheƙa da gudu yă bar tumakin. Sai kyarkecin yă kai wa garken hari, yă kuma watsar da su.
13
Mutumin yakan gudu don shi ɗan haya ne kawai, bai kuwa damu da tumakin ba.
14
“Ni ne makiyayi mai kyau; na san tumakina, tumakina kuma sun san ni,
15
kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uba, ina kuwa ba da raina domin tumakin.
16
Ina da waɗansu tumaki da ba na wannan garken ba ne. Dole ne in kawo su su ma. Za su saurari muryata, za su kasance garke guda ɗaya, makiyayi guda kuma.
17
Abin da ya sa Ubana yake ƙaunata ke nan, domin ina ba da raina, in ɗauko shi kuma.
18
Ba mai karɓe mini rai, ina dai ba da shi. Ina da iko in ba da shi, ina da iko in ɗauko shi kuma. Wannan umarni kuwa daga wurin Ubana na karɓo shi.”
19
Saboda waɗannan kalmomi fa, sai ɓaraka ta sāke shiga cikin Yahudawa.
20
Da yawa daga cikinsu suka ce, “Yana da aljani, yana kuma hauka. Don me za ku saurare shi?”
21
Amma waɗansu suka ce, “Kai, waɗannan kalmomi ba na mai aljani ba ne. Anya, aljani yana iya buɗe idanun makaho?”
22
Bikin Miƙawa a Urushalima ya kewayo, lokacin sanyin hunturu ne kuwa.
23
Sai ga Yesu a filin haikali yana zagawa a Shirayin Solomon,
24
sai Yahudawa suka taru kewaye da shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In kai ne Kiristin, ka faɗa mana a fili mana.”
25
Yesu ya amsa ya ce, “Na faɗa muku, amma ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi cikin sunan Ubana su suke nuna ko wane ne ni.
26
Amma ba ku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne.
27
Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na.
28
Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.
Settings