Ayuba 39:9-25
9
“Ko ɓauna zai yarda yă zauna a wurin sa wa dabbobi abinci? Zai tsaya a ɗakin dabbobinka da dare?
10
Ko za ka iya daure shi da igiya a kwarin kunya? Zai yi maka buɗar gonarka?
11
Ko za ka dogara da shi don yawan ƙarfinsa? Za ka bar masa nauyin aikinka?
12
Ko za ka amince da shi yă kawo maka hatsinka gida yă tattara shi a masussuka?
13
“Fikafikan jimina suna bugawa cike da farin ciki amma ba za su gwada kansu da fikafikan da na shamuwa ba.
14
Tana sa ƙwai nata a ƙasa kuma ta bar su su yi ɗumi a cikin ƙasa,
15
ba tă damu ko za a taka su a fasa su, ko waɗansu manyan dabbobi za su tattake su.
16
Tana tsananta wa ’ya’yanta kamar ba nata ba ba tă damu da wahalar da ta sha ba.
17
Gama Allah bai ba ta hikima ba ko kuma iya fahimta.
18
Duk da haka sa’ad da ta buɗe fikafikanta ta shara da gudu tana yi wa doki da mai hawansa dariya.
19
“Ko kai ne kake ba doki ƙarfinsa kai kake rufe wuyansa da geza mai yawa?
20
Ko kai kake sa shi yă yi tsalle kamar fāra, ba ya jin tsoro sai dai a ji tsoronsa.
21
Yana takawa da ƙarfi yana jin daɗin ƙarfinsa yana shiga filin yaƙi gabagadi.
22
Yana yi wa tsoro dariya ba ya jin tsoron kome; ba ya guje wa takobi.
23
Kwari a baka yana lilo a gabansa kibiya da māshi suna wuce kansa.
24
Yana kartar ƙasa da ƙarfi; ba ya iya tsayawa tsab sa’ad da ya ji busar ƙaho.
25
Da jin ƙarar ƙaho sai ya ce, ‘Yauwa!’ Ya ji ƙanshin yaƙi daga nesa, da ihun shugabannin yaƙi.
Settings