Ayuba 16:6-16
6
“Duk da haka in na yi magana, ba na samun sauƙi; in ma na yi shiru zafin ba ya tafiya.
7
Ba shakka ya Allah ka gajiyar da ni; ka ɓata gidana gaba ɗaya.
8
Ka daure ni, ya kuma zama shaida; yadda na rame sai ƙasusuwa, wannan ya sa ake gani kamar don ni mai zunubi ne shi ya sa.
9
Allah ya kai mini hari ya yi kaca-kaca da ni cikin fushinsa yana cizon haƙoransa don fushin da yake yi da ni; ya zura mini ido.
10
Mutane suka buɗe baki suka yi mini riyar reni; suka yi mini ba’a suka haɗu suka tayar mini.
11
Allah ya bashe ni ga mugayen mutane, ya jefa ni hannun mugaye.
12
Dā ina zamana lafiya kome yana tafiya daidai; amma ya ragargaza ni; ya shaƙe ni a wuya; ya murƙushe ni na zama abin barata gare shi;
13
maharbansa sun kewaye ni. Ba tausayi, ya soke ni a ƙodata har jini ya zuba a ƙasa.
14
Ya ji mini rauni a kai a kai ya auko mini kamar mai yaƙi.
15
“Ina makoki saye da tsummoki na ɓoye fuskata a cikin ƙura.
16
Fuskata ta yi ja don kuka idanuna sun kukumbura;
Settings