Tsallake zuwa abun ciki
Irmiya 7:30-34

Irmiya 7:30-34

30
“ ‘Mutanen Yahuda sun yi mugunta a gabana, in ji Ubangiji. Sun kafa gumakansu masu banƙyama a gidan da ake kira da Sunana suka ƙazantar da shi.
31
Sun gida masujadan Tofet a Kwarin Ben Hinnom don miƙa ’ya’yansu maza da mata a wuta, abin da ban yi umarni ba, ba kuwa yi tunaninsa ba.
32
Saboda haka ku yi hankali, kwanaki suna zuwa in ji Ubangiji, sa’ad da mutane ba za su ƙara kira wurin Tofet ko Kwarin Ben Hinnom ba, amma Kwarin Kisa, gama za su binne matattu a Tofet sai har ba sauran wuri.
33
Sa’an nan gawawwakin wannan mutane za su zama abinci ga tsuntsayen sama da kuma namun jeji, ba za a kuwa sami wani da zai kore su ba.
34
Zan kawo ƙarshen muryar murna da farin ciki da muryar amarya da ango a garuruwan Yahuda da kuma a titunan Urushalima, gama ƙasar za tă zama kufai.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options