Irmiya 44:1-14
1
Wannan maganata zo wa Irmiya game da dukan Yahudawa masu zama a Masar ta Ƙasa, a Migdol, Tafanes da Memfis, da kuma a Masar ta Bisa.
2
“Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa kun ga masifa mai girmar da na kawo a kan Urushalima da kuma a kan dukan garuruwan Yahuda. A yau sun zama hamada da kuma kango
3
saboda muguntar da suka aikata. Sun tsokane ni na yi fushi ta wurin ƙone turare da kuma ta wurin bauta wa waɗansu allolin da su ko ku ko kakanninku ba su taɓa sani ba.
4
Sau da sau na aiki bayina annabawa, waɗanda suka ce, ‘Kada ku yi wannan abin ƙyama da na ƙi!’
5
Amma ba su saurara ko su kasa kunne ba; ba su juye daga muguntarsu ko su daina ƙone turare wa waɗansu alloli ba.
6
Saboda haka, fushina mai ƙuna ya fāɗo a kan garuruwan Yahuda da kuma titunan Urushalima na kuma mai da su kufai da suke a yau.
7
“To, ga abin da Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa don me kuka kawo irin masifa mai girma haka a kanku ta wurin warewa daga Yahuda maza da mata, yara da jarirai, kun kuma bar kanku babu raguwa?
8
Me ya sa kuka tsokane ni in yi fushi saboda abin da hannuwanku suka yi, kuna ƙone turare wa waɗansu alloli a Masar, inda kuka zo don ku zauna? Za ku hallakar da kanku ku kuma mai da kanku abin la’ana da abin zargi da abin ba’a a cikin dukan al’umman duniya.
9
Kun manta mugayen ayyukan kakanninku, da na sarakuna da sarauniyoyin Yahuda da mugayen ayyukanku, da na matanku a cikin Yahuda da kan titunan Urushalima?
10
Har yă zuwa yau ba su ƙasƙantar da kansu ko su nuna bangirma, ko su kiyaye dokata da ƙa’idodin da na sa a gabanku da kakanninku ba.
11
“Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa na ƙudura in aukar muku da masifa in kuma hallaka dukan Yahuda.
12
Zan ɗauke raguwar Yahuda waɗanda suka ƙudurta su je Masar su zauna a can. Duk za su hallaka a Masar; za su mutu ta wurin takobi ko su mutu da yunwa. Daga ƙarami zuwa babba, za su mutu ta wurin takobi ko yunwa. Za su zama abin zarge da abin tsoro, abin la’ana da abin ba’a.
13
Zan hukunta waɗanda suke zama a Masar da takobi, yunwa da annoba, yadda na hukunta Urushalima.
14
Babu wani daga raguwar Yahuda wanda ya tafi Masar da zai kuɓuta ko ya tsira har ya komo zuwa ƙasar Yahuda, wadda za su yi marmari su komo su zauna; babu wani da zai komo sai dai ’yan gudun hijira.”
Settings