Ishaya 8:4-10
4
Kafin yaron yă san yadda zai ce ‘Babana’ ko ‘Mamana,’ sarkin Assuriya zai kwashe arzikin Damaskus da ganimar Samariya.”
5
Ubangiji ya sāke yi mini magana ya ce,
6
“Domin wannan jama’a ta ƙi natsattsen ruwan rafin Shilowa suka yi ta farin ciki a kan Rezin ɗan Remaliya,
7
saboda haka Ubangiji yana shirin yă kawo musu rigyawar ruwan Kogi, wato, sarkin Assuriya da dukan sojojinsa. Zai cika dukan gaɓoɓinsa, yă kuma malala har zuwa bakin kogi.
8
Yă yi ta malala har zuwa cikin Yahuda, yă shafe ta, yana ratsa ta ciki har yă kai kafaɗa. Fikafikansa da ya buɗe za su rufe fāɗin ƙasarka, Ya Immanuwel!”
9
Ku yi kururuwar yaƙi, ku ƙasashe, ku kuma ji tsoro! Ku saurara, dukanku manisantan ƙasashe. Ku shirya don yaƙi, ku kuma ji tsoro!
10
Ku ƙirƙiro dabarunku, amma ba za su yi nasara ba; ku ƙulla shirye-shiryenku, amma ba za su yi amfani ba, gama Allah yana tare da mu.
Settings