Ishaya 63:3-6
3
“Na tattake ’ya’yan inabi ni kaɗai; cikin al’ummai kuma babu wani tare da ni. Na tattake su cikin fushina Na matse su cikin hasalata; jininsu ya fantsamar wa rigunana, na kuma ɓata dukan tufafina.
4
Gama ranar ɗaukan fansa tana a cikin zuciyata, kuma shekarar fansata ta zo.
5
Na duba, amma babu wanda zai taimaka, na yi mamaki cewa ba wanda ya goyi baya; saboda haka hannuna ya yi mini ceto, fushina kuma ya rayar da ni.
6
Na tattake al’ummai cikin fushina; cikin hasalata kuma na sa sun bugu na kuma zub da jininsu a ƙasa.”
Settings