Skip to content
Ishaya 62:10-12

Ishaya 62:10-12

10
Ku wuce, ku wuce ƙofofi! Ku shirya hanya saboda mutane. Ku gina, ku gina babbar hanya! Ku kawar da duwatsu. Ku ɗaga tuta saboda al’ummai.
11
Ubangiji ya yi shela ga iyakokin duniya cewa, “Faɗa wa Diyar Sihiyona, ‘Ga Mai Cetonki yana zuwa! Ga ladarsa tana tare da shi, sakamakonsa yana raka shi.’ ”
12
Za a ce da shi Tsattsarkar Mutane, Fansassu na Ubangiji; za a kuma ce da ke Wadda Aka Nema Birnin da Ba Za a Ƙara Yashe ta ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options