Ishaya 42:1-9
1
“Ga bawana, wanda na ɗaukaka, zaɓaɓɓen nan nawa wanda nake jin daɗi; Zan sa Ruhuna a cikinsa zai kuwa kawo adalci ga al’ummai.
2
Ba zai yi ihu ko ya tā da murya, ko ya daga muryarsa a tituna ba.
3
Iwan da ta tanƙware ba zai karye ba, ba zai kashe lagwani mai hayaƙi ba. Cikin aminci zai kawo adalci;
4
ba zai kāsa ko ya karai ba sai ya kafa adalci a duniya. Cikin dokarsa tsibirai za su sa zuciya.”
5
Ga abin da Allah Ubangiji ya ce, shi da ya halicci sammai ya kuma miƙe su, wanda ya shimfiɗa duniya da dukan abin da ya fito cikinta, wanda ya ba wa mutanenta numfashi, da rai ga waɗanda suke tafiya a kanta.
6
“Ni Ubangiji, na kira ka cikin adalci; zan riƙe hannunka. Zan kiyaye ka in kuma sa ka zama alkawari ga mutane haske kuma ga Al’ummai,
7
don ka buɗe idanun makafi ka ’yantar da kamammu daga kurkuku kuma kunce ɗaurarrun kurkuku masu zama cikin duhu.
8
“Ni ne Ubangiji; sunana ke nan! Ba zan ba da ɗaukakata ga wani ba ko yabona ga gumaka.
9
Duba, abubuwan da sun tabbata, sababbin abubuwa kuwa nake furtawa; kafin ma su soma faruwa na sanar da su gare ku.”
Settings