Ishaya 40:1-11
1
Ta’aziyya, ku ta’azantu mutanena, in ji Allahnku.
2
Yi magana mai kwantar da rai ga Urushalima, ku kuma furta mata cewa aiki mai zafinta ya isa, cewa an fanshi zunubinta, cewa ta karɓi daga hannun Ubangiji ninki biyu saboda dukan zunubanta.
3
Muryar wani tana kira cewa, “A cikin hamada ku shirya hanya saboda Ubangiji; ku miƙe manyan hanyoyi domin Allahnmu a cikin jeji.
4
Za a cike kowane kwari, a baje kowane dutse da kowane tudu; za a mayar da karkatattun wurare su zama sumul, munanan wurare kuma su zama da kyau.
5
Za a kuma bayyana ɗaukakar Ubangiji, dukan mutane kuwa za su gan ta. Gama Ubangiji da kansa ne ya yi magana.”
6
Muryar tana cewa, “Ka yi shela.” Na kuwa ce, “Me zan yi shelar?” “Dukan mutane kamar ciyawa suke, kuma dukan ɗaukakarsu kamar furannin jeji ne.
7
Ciyawa takan yanƙwane, furanni kuma su yi yaushi, domin Ubangiji ya hura iska a kansu. Tabbatacce mutane ciyawa ne.
8
Hakika ciyawa takan yanƙwane, furanni kuma su yi yaushi, amma maganar Allahnmu tana nan daram har abada.”
9
Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Sihiyona, ka haura a bisa dutse. Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Urushalima, ka tā da muryarka ka yi ihu, ka ɗaga ta, kada ka ji tsoro; faɗa wa garuruwan Yahuda, “Ga Allahnku!”
10
Duba, Ubangiji Mai Iko Duka yana zuwa da iko, hannunsa kuma yana yin mulki dominsa. Duba, ladarsa tana tare da shi, sakamakonsa kuma na rakiyarsa.
11
Yakan lura da garkensa kamar makiyayi. Yakan tattara tumaki wuri ɗaya yă riƙe su kurkusa da ƙirjinsa; a hankali kuma yakan bi da masu ba da mama.
Settings