Ishaya 33:1-9
1
Kaitonka, ya kai mai hallakarwa, kai da ba a hallakar da kai ba! Kaitonka, ya maciya amana, kai da ba a ci amanarka ba! Sa’ad da ka daina hallakarwa, za a hallaka ka; sa’ad da ka daina cin amana, za a ci amanarka.
2
Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai; muna marmarinka. Ka zama ƙarfinmu kowace safiya, cetonmu a lokacin damuwa.
3
Da tsawar muryarka, mutane za su gudu; sa’ad da ka tashi, al’ummai za su watse.
4
Ganimarku, ya al’ummai ƙanana fāri sun girbe; kamar tarin fārin da mutane sun fāɗa wa.
5
Ubangiji da girma yake, gama yana zaune a bisa; zai cika Sihiyona cikin gaskiya da adalci.
6
Zai zama tabbataccen harsashi na koyaushe, ma’ajin ceto da hikima da sani a yalwace; tsoron Ubangiji shi ne mabuɗin wannan dukiya.
7
Duba, jarumawansu suna kuka da ƙarfi a tituna; jakadun salama suna kuka mai zafi.
8
An gudu an bar manyan hanyoyi, babu matafiye a kan hanyoyi. Aka keta yarjejjeniya, an rena shaidunsa ba a kuwa ganin girman kowa.
9
Ƙasa tana kuka an kuma gudu an bar ta, Lebanon ta sha kunya ta kuma yanƙwane; Sharon ta zama kamar Araba, Bashan da Karmel sun kakkaɓe ganyayensu.
Settings