Ishaya 33:7-12
7
Duba, jarumawansu suna kuka da ƙarfi a tituna; jakadun salama suna kuka mai zafi.
8
An gudu an bar manyan hanyoyi, babu matafiye a kan hanyoyi. Aka keta yarjejjeniya, an rena shaidunsa ba a kuwa ganin girman kowa.
9
Ƙasa tana kuka an kuma gudu an bar ta, Lebanon ta sha kunya ta kuma yanƙwane; Sharon ta zama kamar Araba, Bashan da Karmel sun kakkaɓe ganyayensu.
10
“Yanzu zan tashi,” in ji Ubangiji. “Yanzu ne za a ɗaukaka ni; yanzu za a ɗaga ni sama.
11
Kun yi cikin yayi, kuka haifi kara; numfashinku wuta ne da zai cinye ku.
12
Za a ƙone mutane kamar da ƙuna farar ƙasa; kamar ƙayayyuwan da aka sare aka kuma sa musu wuta.”
Settings