Skip to content
Hosiya 6:7-10

Hosiya 6:7-10

7
Kamar Adamu, sun tā da alkawari, sun yi mini rashin aminci a can.
8
Gileyad birni ce ta mugayen mutane, da tabon alamun jini.
9
Kamar yadda mafasa sukan yi fakon mutum, haka ƙungiyoyin firistoci suke; suna kisa a hanya zuwa Shekem, suna aikata laifofi bankunya.
10
Na ga wani abu mai bantsoro a gidan Isra’ila. A can Efraim ya miƙa wuya ga karuwanci Isra’ila kuma ta ƙazantu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options