Hosiya 6:4-6
4
“Me zan yi da kai Efraim? Me zan yi da kai Yahuda? Ƙaunarku tana kamar hazon safiya, kamar raɓar safiya da takan ɓace.
5
Saboda haka na yayyaga ku kucu-kucu tare da annabawana, na kashe ku da kalmomin bakina; hukuntaina sun haskaka kamar walƙiya a kanku.
6
Gama jinƙai nake bukata, ba hadaya ba, ku kuma san Allah a maimakon hadayun ƙonawa.
Settings