Tsallake zuwa abun ciki
Farawa 6:5-13

Farawa 6:5-13

5
Ubangiji kuwa ya lura cewa muguntar mutum ta yi yawa a duniya, kuma kowane abin da yake tunani a zuciyarsa mugu ne kawai a kowanne lokaci.
6
Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya zafe shi ƙwarai.
7
Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan kawar da mutum, da dabbobi, da halittu masu rarrafe a ƙasa da kuma tsuntsayen sama waɗanda na halitta, daga doron ƙasa, saboda na damu da na yi su.”
8
Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.
9
Ga tarihin Nuhu. Nuhu mutum ne mai adalci, marar abin zargi a cikin mutanen zamaninsa, ya kuma yi tafiya tare da Allah.
10
Nuhu yana da ’ya’ya maza uku, Shem, Ham da Yafet.
11
Duniya dai ta lalace sosai a gaban Allah, ta kuma cika da tashin hankali.
12
Allah ya ga yadda duniya ta lalace, gama dukan mutane a duniya sun lalatar da rayuwarsu.
13
Saboda haka, Allah ya ce wa Nuhu, “Zan kawo ƙarshen dukan mutane, gama saboda su duniya ta cika da tashin hankali. Lalle zan hallaka su da kuma duniya.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options