Farawa 37:3-11
3
Isra’ila dai ya fi ƙaunar Yusuf fiye da kowanne a cikin sauran ’ya’yansa maza, gama an haifa masa shi a cikin tsufansa. Sai ya yi masa riga mai gwanin kyau.
4
Sa’ad da ’yan’uwansa suka ga cewa mahaifinsu ya fi ƙaunarsa fiye da kowanne daga cikinsu, sai suka ƙi jininsa, ba sa kuma maganar alheri da shi.
5
Sai Yusuf ya yi mafarki, sa’ad da ya faɗa wa ’yan’uwansa, suka ƙara ƙin jininsa.
6
Ya ce musu, “Ku saurari wannan mafarkin da na yi.
7
Muna daurin dammunan hatsi a gona, sai nan da nan damina ya tashi ya tsaya, yayinda dammunanku suka taru kewaye da nawa suka rusuna masa.”
8
Sai ’yan’uwansa suka ce masa, “Kana nufin za ka yi mulki a kanmu ke nan? Ko kuwa za ka zama sarki, a bisanmu?” Suka ƙara ƙin jininsa saboda mafarkinsa da kuma abin da ya faɗa.
9
Sai Yusuf ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa ’yan’uwansa. Ya ce, “Ku saurara, na sāke yin wani mafarki, a wannan lokaci, na ga rana da wata da taurari goma sha ɗaya suna rusuna mini.”
10
Sa’ad da ya faɗa wa mahaifinsa da kuma ’yan’uwansa, sai mahaifinsa ya kwaɓe shi ya ce, “Wanne irin mafarki ne haka da ka yi? Kana nufin ni da mahaifiyarka da ’yan’uwanka za mu zo gabanka mu rusuna maka?”
11
’Yan’uwansa suka yi kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe batun nan a zuciya.
Settings