Skip to content
Farawa 27:30-45

Farawa 27:30-45

30
Bayan Ishaku ya gama sa masa albarka, Yaƙub yana fita daga mahaifinsa ke nan, sai ga ɗan’uwansa Isuwa ya dawo daga farauta.
31
Shi ma ya shirya abinci mai daɗi ya kawo wa mahaifinsa. Sa’an nan ya ce masa, “Babana, tashi ka zauna ka ci daga abin da na farauto, domin ka sa mini albarka.”
32
Mahaifinsa Ishaku ya tambaye shi, “Wane ne kai?” Ya amsa, “Ni ne ɗanka, ɗan farinka, Isuwa.”
33
Ishaku ya yi makyarkyata ƙwarai ya ce, “To, wane ne wannan da ya farauto nama ya kawo mini kafin ka zo, har na ci na kuma sa masa albarka? Tabbatacce zai zama mai albarka!”
34
Sa’ad da Isuwa ya ji kalmomin mahaifinsa, sai ya fashe da kuka mai zafi kuma da ƙarfi, ya ce wa mahaifinsa, “Ka albarkace ni, ni ma, baba!”
35
Amma ya ce, “Ɗan’uwanka ya zo da makirci ya karɓi albarkarka.”
36
Isuwa ya ce, “Ba saboda haka ne aka raɗa masa suna Yaƙub ba? Ya yi mini ƙwace sau biyu ke nan; ya ƙwace mini matsayina na ɗan fari, ga shi yanzu kuma ya karɓi albarkata.” Sa’an nan ya yi tambaya, “Ba sauran albarkar da ka rage mini?”
37
Ishaku ya amsa wa Isuwa, “Na mai da shi shugaba a kanka, na sa dukan dangoginsa su zama bayinsa, na kuma ba shi hatsi da sabon ruwan inabi. Saboda haka me kuma zan yi maka ɗana?”
38
Isuwa ya ce wa mahaifinsa, “Iyakar albarkar da kake da ita ke nan, baba? Ka albarkace ni ni ma, baba!” Sai Isuwa ya ɗaga murya ya yi kuka.
39
Mahaifinsa Ishaku ya amsa masa ya ce, “Ga shi, ni’imar ƙasar za tă nisanci mazauninka. Raɓar samaniya can ƙwanƙoli za tă nisance ka.
40
Za ka rayu ta wurin takobi za ka kuwa bauta wa ɗan’uwanka. Amma sa’ad da ka ɓalle, za ka kakkarye karkiyarsa daga wuyanka.”
41
Isuwa ya riƙe Yaƙub a zuciya saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Ya ce wa kansa, “Kwanakin mutuwar mahaifina sun yi kusa; sa’an nan zan kashe ɗan’uwana Yaƙub.”
42
Sa’ad da aka faɗa wa Rebeka abin da babban ɗanta Isuwa ya faɗa, sai ta kira ɗanta Yaƙub ta ce masa, “Ɗan’uwanka Isuwa yana ta’azantar da kansa da tunanin kashe ka.
43
To, fa, ɗana, yi abin da na ce; gudu nan take zuwa wurin ɗan’uwana Laban a Haran.
44
Zauna tare da shi na ɗan lokaci sai ɗan’uwanka ya huce.
45
Sa’ad da ɗan’uwanka ya daina fushi da kai, ya kuma manta da abin da ka yi masa, zan aika don ka dawo daga can. Don me zan rasa ku biyu a rana guda?”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options