Galatiyawa 5:1-12
1
Saboda ’yanci ne Kiristi ya ’yantar da mu. Sai ku tsaya daram, kada ku yarda ku sāke komawa ƙarƙashin nauyin bauta.
2
Ku lura da kalmomina! Ni Bulus ina gaya muku cewa in kuka yarda aka yi muku kaciya, wannan ya nuna Kiristi ba shi da amfani a gare ku ba ko kaɗan.
3
Haka kuma ina ƙara sanar wa kowane mutumin da ya yarda aka yi masa kaciya cewa dole yă kiyaye dukan Doka.
4
Ku da kuke ƙoƙarin kuɓuta ta wurin Doka an raba ku da Kiristi ke nan; kuka kuma fāɗi daga alheri.
5
Amma ta wurin bangaskiya muna marmarin jira adalcin da muke bege ta wurin Ruhu.
6
Gama a cikin Kiristi Yesu, kaciya ko rashin kaciya ba su da wani amfani. Abin da kawai yake da amfani shi ne, bangaskiyar da take bayyana kanta ta wurin ƙauna.
7
Kun yi tsere mai kyau a dā. Wa ya shige gabanku ya hana ku bin gaskiya?
8
Wannan rarrashin da ake muku ba daga wanda ya kira ku ba ne.
9
“Ɗan yisti kaɗan ne yake gama dukan curin burodi.”
10
Ina da tabbaci cikin Ubangiji cewa ba za ku bi wani ra’ayi dabam ba. Wannan da yake rikita ku za a hukunta shi, ko shi wane ne.
11
’Yan’uwa, da a ce har yanzu ina wa’azin kaciya ne, to, me ya sa ake tsananta mini har yanzu? In haka ne, ashe, an kawar da abin da yake sa tuntuɓe game da gicciye ke nan.
12
Da ma a ce masu tā da hankalinku ɗin nan su yanke gabansu gaba ɗaya mana!
Settings