Ezra 8:1-20
1
Waɗannan su ne shugabannin iyalai, da kuma waɗanda suka dawo tare da ni daga Babilon a zamanin mulkin Sarki Artazerzes.
2
Daga zuriyar Finehas, Gershom ne shugaba; daga zuriyar Itamar, Daniyel ne shugaba; daga zuriyar Dawuda, Hattush
3
ɗan zuriyar Shekaniya ne shugaba, daga zuriyar Farosh, Zakariya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 150;
4
daga Fahat-Mowab, Eliyehoyenai ɗan Zerahiya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 200;
5
daga zuriyar Zattu, Shekaniya ɗan Yahaziyel ne shugaba, tare da shi akwai mutum 300;
6
daga zuriyar Adin, Ebed ɗan Yonatan ne shugaba, tare da shi akwai mutum 50;
7
daga zuriyar Elam, Yeshahiya ɗan Ataliya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 70;
8
daga zuriyar Shefatiya, Zebadiya ɗan Mika’ilu ne shugaba, tare da shi akwai mutum 80;
9
daga iyalin Yowab, Obadiya ɗan Yehiyel ne shugaba, tare da shi akwai mutum 218;
10
daga Bani, Shelomit ɗan Yosifiya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 160;
11
daga Bebai, Zakariya ɗan Bebai ne shugaba, tare da shi akwai mutum 28;
12
daga iyalin Azgad, Yohanan ɗan Hakkatan ne shugaba, tare da shi akwai mutum 110;
13
zuriya ta Adonikam ne suka zo daga ƙarshe, sunayensu kuwa su ne Elifelet, Yehiyel da Shemahiya, tare da su akwai mutum 60;
14
daga zuriyar Bigwai, Uttai da Zakkur ne shugabanni, tare da su akwai mutum 70.
15
Na kuma tattara su a bakin rafi wanda yake gangarawa zuwa Ahawa, muka kafa sansani a can kwana uku. Da na bincika cikin mutane da firistoci, sai na tarar babu Lawiyawa.
16
Saboda haka sai na aika a kira Eliyezer, da Ariyel, da Shemahiya, da Elnatan, da Yarib, da Natan, da Zakariya, da Meshullam waɗanda su ne shugabanni. Na kuma sa a kira Yohiyarib da Elnatan waɗanda masana ne.
17
Na sa su je wurin Iddo wanda yake shugaba a Kasifiya. Aka gaya musu abin da za su gaya wa Iddo da ’yan’uwansa masu aiki a haikali a Kasifiya don su aiko mana waɗanda za su yi mana hidima a haikalin Allahnmu.
18
Da yake Allah yana tare da mu, sai suka aiko mana da Sherebiya, wanda ya iya aiki, shi daga zuriyar Mali ɗan Lawi ne, ɗan Isra’ila. Sai ya zo tare da ’ya’yansa da kuma ’yan’uwansa. Dukansu dai mutum 18 ne.
19
Suka kuma aika da Hashabiya tare da Yeshahiya daga zuriyar Merari, da ’yan’uwansu da kuma ’ya’yansu, su kuma mutum 20 ne.
20
Sun kuma kawo masu aiki a haikali mutum 220, ƙungiyar da Dawuda da abokan aikinsa suka keɓe don su taimaki Lawiyawa aiki. Duk aka rubuta waɗannan da sunayensu.
Settings