Ezra 3:8-13
8
A wata na biyu na shekara ta biyu, bayan sun komo gidan Allah a Urushalima, sai Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, Yoshuwa ɗan Yozadak da sauran ’yan’uwansa (Firistoci da Lawiyawa da duk waɗanda suka komo Urushalima daga bauta) suka fara aiki, aka zaɓi Lawiyawa daga masu shekaru ashirin da haihuwa zuwa waɗanda suka wuce haka don su dubi aikin ginin gidan Ubangiji.
9
Yeshuwa da ’ya’yansa maza, da ’yan’uwansa, da Kadmiyel da ’ya’yan Yahuda (’yan zuriyar Hodawiya), da ’ya’yan Henadad, da ’ya’yansu da ’yan’uwansu, dukansu Lawiyawa ne, suka haɗa kai cikin duban masu aikin gidan Allah.
10
Da masu ginin suka aza harsashin ginin haikalin Ubangiji, sai firistoci suka sa kayansu na firistoci suka riƙe ƙahonin busa, Lawiyawa (’ya’yan Asaf) kuwa suka riƙe kuge, suka yi shiri domin su rera yabo ga Ubangiji kamar yadda Dawuda Sarkin Isra’ila ya ba da umarni.
11
Suka rera waƙar yabo da godiya ga Ubangiji, suna cewa, “Shi nagari ne; ƙaunarsa kuwa ga Isra’ila har abada ce.” Dukan jama’a kuwa suka yabi Ubangiji da murya mai ƙarfi, domin an aza harsashin ginin gidan Ubangiji.
12
Amma tsofaffin firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin iyalai da yawa, waɗanda dā suka ga yadda haikali na farko yake, suka fashe da kuka mai ƙarfi sa’ad da suka ga an aza harsashin ginin wannan haikali, yayinda waɗansu kuma suka yi ihu da farin ciki.
13
Ba wanda zai iya rabe tsakanin ihun farin ciki da na kuka, domin mutanen sun tā da murya sosai har aka ji su daga nesa.
Settings