Skip to content
Ezra 10:18-24

Ezra 10:18-24

18
A cikin zuriyar firistoci, ga waɗanda suka auri mata baƙi. Daga zuriyar Yeshuwa ɗan Yozadak da ’yan’uwansa, akwai Ma’asehiya, da Eliyezer, da Yarib, da Gedaliya.
19
(Su ne suka miƙa hannuwansu suka nuna sun yarda su kori matansu baƙi, kowannensu kuma ya ba da rago daga cikin garkensa don a miƙa hadaya don zunubi.)
20
Daga zuriyar Immer, akwai Hanani da Zebadiya.
21
Daga zuriyar Harim, akwai Ma’asehiya, Iliya, Shemahiya, Yehiyel da Uzziya.
22
Daga zuriyar Fashhur, akwai Eliyohenai, Ma’asehiya, Ishmayel, Netanel, Yozabad da Eleyasa.
23
Cikin Lawiyawa, akwai Yozabad, Shimeyi, Kelaya (wato, Kelita), Fetahahiya, Yahuda, Eliyezer.
24
Daga mawaƙa, akwai Eliyashib. Daga masu tsaron ƙofofin haikali, akwai Shallum, Telem da Uri.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options