Skip to content
Ezekiyel 44:12-31

Ezekiyel 44:12-31

12
Amma domin sun yi musu hidima a gaban gumakansu suka sa gidan Isra’ila ya yi zunubi, saboda haka na ɗaga hannu na rantse cewa dole su ɗauki alhakin zunubinsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
13
Ba za su yi kusa don su yi hidima kamar firistoci ko su zo kusa da abubuwana masu tsarki ko hadayuna mafi tsarki ba; dole su sha kunya saboda ayyukansu na banƙyama.
14
Duk da haka zan sa su su lura da ayyukan haikali da kuma dukan ayyukan da za a yi a cikinsa.
15
“ ‘Amma firistoci, waɗanda suke Lawiyawa kuma zuriyar Zadok waɗanda suka yi aminci ta wurin yin ayyukansu a wurina mai tsarki sa’ad da Isra’ilawa suka kauce daga gare ni, su ne za su zo kusa don hidima a gabana; za su tsaya a gabana don miƙa hadayun kitse da jini, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
16
Su ne kaɗai za su shiga wurina mai tsarki; su ne kaɗai za su zo kusa da teburina don yin hidima a gabana su kuma yi hidimata.
17
“ ‘Sa’ad da suka shiga ƙofofin fili na can ciki, dole su sa tufafin lilin; kada su sa wani rigar da aka yi da ulu yayinda suke hidima a ƙofofin fili na can ciki da cikin haikali.
18
Za su naɗa rawunan lilin a kawunansu, su kuma sa wandunan lilin. Kada su sa wani abin da zai sa su yi zuffa.
19
Sa’ad da suka fita daga haikali zuwa fili na waje inda mutane suke, sai su tuɓe rigunan da suka yi hidima da su su bar su a tsarkakan ɗakuna, su sa waɗansu riguna, don kada su tsarkake mutane ta wurin rigunansu.
20
“ ‘Ba za su aske kawunansu ko su bar gashin kansu ya yi tsayi ba, amma sai su sausaye gashin kansu.
21
Kada firist ya sha ruwan inabi sa’ad da zai shiga fili na can ciki.
22
Kada su auri gwauruwa ko macen da aka sāke; za su auri budurwai ne kaɗai na Isra’ilawa ko gwaurayen firistoci.
23
Za su koyar da mutanena bambanci tsakanin tsarki da rashin tsarki su kuma nuna musu yadda za su bambanta marar tsarki da mai tsarki.
24
“ ‘A duk wani rashin jituwa, firistoci za su zama alƙalai su kuma yanke magana bisa ga farillaina. Za su kiyaye dokokina da ƙa’idodina a dukan ƙayyadaddun bukukkuwana, su kuma kiyaye Asabbataina da tsarki.
25
“ ‘Firist ba zai ƙazantar da kansa ta wurin zuwa kusa da gawa ba; amma, in gawar mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ko ɗansa ko ’yarsa, ko ɗan’uwansa ko ’yar’uwarsa ce, to, ba zai ƙazantar da kansa ba.
26
Bayan ya tsarkaka, dole yă jira har kwana bakwai.
27
A ranar da ya shiga fili na can ciki na wuri mai tsarki don hidima a wuri mai tsarki, zai miƙa hadaya don zunubi saboda kansa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
28
“ ‘Ni ne kaɗai zan zama abin gādon da firistoci za su kasance da shi. Kada ka ba su wani mallaka a Isra’ila; zan zama mallakarsu.
29
Za su ci hadaya ta gari, hadaya don zunubi da hadaya don laifi; da kuma kowane keɓaɓɓen abu a Isra’ila da za a ba wa Ubangiji zai zama nasu.
30
Mafi kyau na nunan farinku da kuma dukan kyautanku na musamman za su zama na firistoci. Za ku ba su rabo na fari na ɓarzajjen hatsinku saboda albarka ta kasance a gidanku.
31
Firistoci ba za su ci mushen tsuntsu ko na dabba ba, ba kuwa za su ci waɗanda namun jeji suka kashe ba.

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options