Skip to content
Fitowa 8:16-28

Fitowa 8:16-28

16
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Miƙa hannunka ka bugi ƙurar ƙasa,’ dukan ƙurar ƙasar Masar kuwa za tă zama ƙwari masu cizo.”
17
Suka yi haka, da Haruna ya miƙa hannunsa da sandan, ya bugi ƙurar ƙasa, sai ƙwari masu cizo suka fito a kan mutane da dabbobi. Dukan ƙurar, ko’ina a ƙasar Masar ta zama cinnaku.
18
Sa’ad da bokayen Fir’auna suka yi ƙoƙari yin sihiri iri na rufe ido domin su fito da kwari, sai suka kāsa. Ƙwari masu cizo kuwa suka rufe mutane da dabbobi.
19
Sai bokaye suka ce wa Fir’auna, “Wannan fa da hannun Allah a ciki.” Amma zuciyar Fir’auna ta taurare, bai kuwa saurara ba, kamar dai yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.
20
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tashi da sassafe ka sadu da Fir’auna a lokacin da za shi kogi, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, bari mutanena su tafi, don su yi mini sujada.
21
In ba ka bar mutanena suka tafi ba, zan turo da tarin ƙuda a kanka da bayinka, a kan mutanenka da cikin gidajenka. Gidajen Masarawa za su cika da ƙudaje, har ma da ƙasa inda za su taka.
22
“ ‘Amma zan keɓe yankin Goshen, inda mutanena suke don kada ƙudaje su taɓa wurin, domin ka sani cewa Ni, Ubangiji, ina cikin wannan ƙasa.
23
Zan sa iyaka tsakanin jama’ata da jama’arka. Gobe ne wannan mu’ujiza za tă auku.’ ”
24
Ubangiji kuwa ya yi haka. Tarin ƙuda suka zubo a fadar Fir’auna da cikin gidajen bayinsa, da ko’ina a Masar, ƙasar kuwa ta lalace saboda ƙudaje.
25
Sai Fir’auna ya kira Musa da Haruna ya ce, “Ku tafi, ku miƙa hadaya ga Allahnku, a nan a cikin ƙasar.”
26
Amma Musa ya ce, “Wannan ba zai yiwu ba. Hadayun da mukan miƙa wa Ubangiji, Allahnmu haram ne ga Masarawa. In kuwa muka miƙa hadayun da suke haram a idanunsu, ba za su jajjefe mu ba?
27
Dole mu yi tafiya kwana uku cikin hamada domin miƙa hadayu ga Ubangiji Allahnmu, yadda ya umarce mu.”
28
Fir’auna ya ce, “Zan bar ku ku tafi, don ku miƙa hadayu ga Ubangiji Allahnku, a cikin hamada, amma ba za ku tafi da nisa ba. Yanzu ku yi mini addu’a.”
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options