Skip to content
Fitowa 29:1-26

Fitowa 29:1-26

1
“Ga abin da za ka yi don ka keɓe su, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Ka ɗauki ɗan bijimi da raguna biyu marasa lahani.
2
Daga garin alkama mai laushi marar yisti kuwa, ka yi burodi, da wainan da aka kwaɓa da mai, da ƙosai waɗanda an barbaɗa mai a kai.
3
Ka sa waɗannan a cikin kwando. Sa’an nan ka miƙa su tare da ɗan bijimin da ragunan nan biyu.
4
Bayan haka sai ka kawo Haruna da ’ya’yansa a ƙofar Tentin Sujada ka yi musu wanka.
5
Ka ɗauki rigar ka sa wa Haruna, ka sa masa doguwar rigar, da rigar efod, da efod kanta, da ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Ka ɗaura masa efod da ɗamarar da aka yi mata ado.
6
Ka naɗa masa rawani a kai, ka kuma sa kambi mai tsarki a bisa rawanin.
7
Ka ɗauki man shafewa ka shafe shi, ta wurin zuba man a kansa.
8
Ka kawo ’ya’yansa, ka sa musu taguwoyi,
9
ka kuma sa musu huluna a kansu. Sa’an nan ka ɗaura wa Haruna da ’ya’yansa abin ɗamara. Su kuwa da zuriyarsu, aikin firist kuwa zai zama nasu ta wurin dawwammamiyar farilla. “Ta haka za ka keɓe Haruna da ’ya’yansa maza.
10
“Ka kuma kawo bijimin a gaban Tentin Sujada, sai Haruna da ’ya’yansa su ɗora hannuwansu a kansa.
11
Ka yanka shi a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada.
12
Ka ɗibi jinin bijimin ka zuba a kan ƙahoni na bagade da yatsanka, sauran jinin kuwa ka zuba a gindin bagaden.
13
Sa’an nan ka ɗauki dukan kitsen da ya rufe kayan ciki, da kitsen da yake manne da hanta, da ƙoda biyu da kuma kintsen da yake a kansu, ka ƙone su a kan bagade.
14
Amma ka ƙone naman bijimin, da fatarsa, da kayan cikin, a bayan sansani. Hadaya ce ta zunubi.
15
“Ka ɗauki ɗaya daga cikin ragunan, Haruna kuwa da ’ya’yan maza za su ɗora hannuwansa a kansa.
16
Ka yanka ragon, ka ɗibi jinin, ka yayyafa shi kewaye da gefen bagaden.
17
Ka yayyanka rago gunduwa-gunduwa, ka wanke kayan cikin, da ƙafafun, da kan, ka haɗa su da gunduwoyin.
18
Sa’an nan ka ƙone ragon ɗungum a kan bagade. Hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji, mai daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
19
“Ka ɗauki ɗayan ragon, sai Haruna da ’ya’yansa maza su ɗora hannuwansu a kansa.
20
Ka yanka ragon, ka ɗibi jinin, ka shafa a bisa leɓen kunnen Haruna na dama, da bisa leɓen kunnuwan ’ya’yansa maza na dama, da kan manyan yatsotsin hannuwansu na dama, da kuma a kan manyan yatsotsin ƙafafunsu na dama. Sauran jinin kuwa, sai ka yayyafa shi kewaye da gefen bagaden.
21
Ka ɗibi jinin da yake a kan bagade, da man shafewa, ka yafa a kan Haruna da rigunansa, da kuma a kan ’ya’yansa maza da rigunansu. Sa’an nan shi da ’ya’yansa maza da rigunansu za su tsarkake.
22
“Ka ɗebi kitse daga wannan rago, ka yanke wutsiyarsa mai kitse, ka kuma ɗebi kitsen da ya rufe kayan ciki, da kitsen da yake bisa hanta, da ƙoda biyu da kitsen da yake kansu, da cinyar dama. (Gama rago ne don naɗi.)
23
Daga kwandon burodi marar yisti, wanda yake gaban Ubangiji, ka ɗauki dunƙule ɗaya, da waina da aka yi da mai, da kuma ƙosai.
24
Ka sa dukan waɗannan a hannun Haruna da ’ya’yansa maza, su kaɗa su a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa.
25
Sa’an nan ka karɓe su daga hannuwansu, ka ƙone su a kan bagade tare da hadaya ta ƙonawa, domin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
26
Bayan haka, ka ɗauki ƙirjin ragon domin naɗin Haruna, ka kaɗa shi a gaban Ubangiji kamar hadaya ta kaɗawa. Wannan ƙirji zai zama rabonka.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options