Skip to content
Fitowa 1:8-16

Fitowa 1:8-16

8
Sai wani sabon sarki wanda bai san Yusuf ba, ya hau sarautar Masar.
9
Ya ce wa mutanensa, “Duba Isra’ilawa sun yi yawa, sun fi ƙarfinmu.
10
Ku zo, mu yi dabara a kansu, in ba haka ba za su ƙaru fiye da haka, in kuwa yaƙi ya tashi tsakaninmu da abokan gāba, za su iya haɗa kai da abokan gāba, su yaƙe mu, su bar ƙasar.”
11
Saboda haka sai suka naɗa shugabannin gandu a kansu don su wahalshe su, su kuma bauta musu, suka sa su suka gina biranen Fitom da Rameses su zama biranen ajiya, domin Fir’auna.
12
Amma duk da wannan ƙarin wulaƙancin da ake yi musu, su kuwa sai daɗa riɓaɓɓanya suke ta yi. Sai tsoron Isra’ilawa ya ƙaru a zuciyar Masarawa,
13
ganin haka sai Masarawa suka ƙara musu wahala.
14
Suka baƙanta wa Isra’ilawa rai da bauta mai wuya, ta wurin sa su yin tubali da yumɓu, da kuma kowace irin bauta a gonaki. A cikin dukan ayyukansu, Masarawa ba su ji tausayinsu ba ko kaɗan.
15
Sai Sarkin Masar ya gaya wa ungozomomin matan Ibraniyawa, wato, su Shofra da Fuwa ya ce,
16
“Sa’ad da kuke taimakon matan Ibraniyawa lokacin haihuwa, in jaririn namiji ne ku kashe shi, amma in ta mace ce, ku bar ta da rai.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options