Afisawa 5:4-21
4
Haka ma bai kamata a sami datti, ƙazamar magana, ko zancen banza a cikinku ba, domin ba su dace ba, a maimakon haka sai ku yi ta yin godiya.
5
Ku dai tabbata, ba wani mai fasikanci, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayin (wanda shi da mai bautar gumaka ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Kiristi da na Allah.
6
Kada wani yă ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya.
7
Saboda haka kada ku haɗa kai da su.
8
Gama a dā zukatanku sun cika da duhu, amma yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi rayuwa kamar ’ya’yan haske
9
(domin amfanin haske ya ƙunshi nagarta, adalci, da kuma gaskiya)
10
ku nemi abin da zai gamshi Ubangiji.
11
Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su.
12
Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da marasa biyayya suke yi a ɓoye.
13
Duk abin da aka kawo a gaban haske ana iya ganinsa, kuma duk abin da aka haskaka yakan zama haske.
14
Shi ya sa aka ce, “Ka farka, ya kai mai barci, ka tashi daga matattu, Kiristi kuwa zai haskaka ka.”
15
Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima.
16
Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne.
17
Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji.
18
Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu.
19
Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji.
20
Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.
21
Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke nuna wa Kiristi.
Settings