Skip to content
Maimaitawar Shari’a 32:15-33

Maimaitawar Shari’a 32:15-33

15
Yeshurun ya yi ƙiba, ya yi kauri; cike da abinci, ya zama da nauyi, ya kuma zama sumul. Ya yashe Allahn da ya yi shi, ya ƙi Dutse Cetonsa.
16
Suka sa shi kishi saboda baƙin allolinsu, suka husata shi da gumakan banƙyamarsu.
17
Suka yi hadaya ga aljanu, waɗanda ba Allah ba, ga allolin da ba su sani ba, ga allolin da aka shigo da su daga baya, allolin da kakanninku ba su ji tsoronsu ba.
18
Kuka rabu da Dutsen da ya zama mahaifi gare ku; kuka manta da Allahn da ya haife ku.
19
Ubangiji ya ga wannan ya kuma ƙi su, domin ’ya’yansa maza da mata sun husata shi.
20
Ya ce, “Zan ɓoye fuskata daga gare su, in ga ƙarshensu; gama su muguwar tsara ce, ’ya’ya ne marasa aminci.
21
Sun sa ni kishi ta wurin abin da ba allah ba, suka kuma husata ni da gumakansu na wofi. Zan sa su yi kishi ta wurin waɗanda ba mutane ba; zan sa su yi fushi ta wurin al’ummar da ba ta da sani.
22
Gama fushina ya kama wuta, tana ci har ƙurewar zurfin lahira. Za tă cinye duniya da girbinta, tă kuma sa wuta a tussan duwatsu.
23
“Zan tula masifu a kansu in kuma gama kibiyoyina a kansu.
24
Zan aika da yunwa mai tsanani a kansu, zazzaɓi mai zafi da muguwar annoba; zan aika da haƙoran namun jeji a kansu, da dafin mesa masu ja da ciki.
25
Waɗanda suke a waje, takobi zai kashe su, a cikin gidajensu kuma tsoro zai mamaye su. ’Yan maza da ’yan mata za su hallaka, haka ma jarirai da maza masu furfura.
26
Na ce zan watsar da su in sa a manta da su a tunanin ’yan adam.
27
Amma ina tsoron tsokanar abokin gāba, don kada abokan gāba su kāsa ganewa har su ce, ‘Hannunmu ne ya yi nasara; ba Ubangiji ne ya aikata dukan wannan ba.’ ”
28
Al’ummai ne marasa azanci, babu ganewa a cikinsu.
29
A ce su masu hikima ne har su gane wannan su gane abin da ƙarshensu zai zama!
30
Yaya mutum guda zai kore dubu, mutum biyu su sa dubu goma su gudu, sai ko Dutsensu ya sayar da su, sai ko Ubangiji ya bashe su.
31
Gama dutsensu ba kamar Dutsenmu ba ne, abokan gābanmu sun san da haka.
32
Kuringarsu ta fito daga kuringar Sodom ne, daga gonakin Gomorra kuma. ’Ya’yan inabinsu dafi ne, nonnansu masu ɗaci ne.
33
Ruwan inabinsu dafin macizai ne, mugun dafin gamshaƙa ne.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options