Skip to content
Maimaitawar Shari’a 22:1-9

Maimaitawar Shari’a 22:1-9

1
In kun ga saniya ko tunkiyar ɗan’uwanku wadda ta ɓace, kada ku ƙyale ta, amma ku tabbata kun komar da ita gare shi.
2
In ɗan’uwan ba ya zama kusa da ku, ko kuwa ba ku san shi ba, sai ku kai ta gida ku ajiye ta sai ya zo nemanta. Sa’an nan ku ba shi ita.
3
Ku yi haka in kun sami jakin ɗan’uwanku, ko rigarsa, ko kowane abin da ya ɓace. Kada ku ƙyale shi.
4
In kuka ga jakin ɗan’uwanku, ko saniyarsa ya fāɗi a kan hanya, kada ku ƙyale shi. Ku taimaka, ku tā da shi.
5
Kada mace ta sa suturar maza, kada kuma namiji ya sa suturar mata, gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamar duk mai yin haka.
6
In kuka ga gidan tsuntsu kusa da hanya, ko a kan itace, ko kuma a ƙasa, mahaifiyar tsuntsun kuwa tana kwance a kan ’ya’yanta, ko kuwa a kan ƙwanta, kada ku kama mahaifiyar duk da ’ya’yan.
7
Za ku iya kwashe ’ya’yan, amma ku tabbata kun bar mahaifiyar tă tafi. Yin haka zai sa ku sami zaman lafiya da tsawon rai.
8
Sa’ad da kuka gina sabon gida, ku ja masa dakali kewaye da rufinku don kada ku jawo laifin zub da jini a kan gidanku in wani ya fāɗi daga kan rufin.
9
Kada ku shuka iri biyu a gonar inabinku; in kuka yi haka, ba abin da kuka shuka ne kaɗai zai ƙazantu ba, amma har da inabinku ma.

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options