Maimaitawar Shari’a 22:5-12
5
Kada mace ta sa suturar maza, kada kuma namiji ya sa suturar mata, gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamar duk mai yin haka.
6
In kuka ga gidan tsuntsu kusa da hanya, ko a kan itace, ko kuma a ƙasa, mahaifiyar tsuntsun kuwa tana kwance a kan ’ya’yanta, ko kuwa a kan ƙwanta, kada ku kama mahaifiyar duk da ’ya’yan.
7
Za ku iya kwashe ’ya’yan, amma ku tabbata kun bar mahaifiyar tă tafi. Yin haka zai sa ku sami zaman lafiya da tsawon rai.
8
Sa’ad da kuka gina sabon gida, ku ja masa dakali kewaye da rufinku don kada ku jawo laifin zub da jini a kan gidanku in wani ya fāɗi daga kan rufin.
9
Kada ku shuka iri biyu a gonar inabinku; in kuka yi haka, ba abin da kuka shuka ne kaɗai zai ƙazantu ba, amma har da inabinku ma.
10
Kada ku haɗa bijimi da jaki su yi noma tare.
11
Kada ku sa rigar ulu da aka gauraye da lilin aka saƙa.
12
Ku yi tuntu a kusurwan huɗu na rigar da kuke sa.
Settings