Skip to content
Ayyukan Manzanni 9:31

Ayyukan Manzanni 9:31

Ana nuna aya 31 tare da mahallin da ke kewaye.
28
Saboda haka Shawulu ya zauna tare da su yana kai da kawowa a sake a cikin Urushalima, yana magana gabagadi a cikin sunan Ubangiji.
29
Ya yi magana ya kuma yi muhawwara da Yahudawa masu jin Hellenanci, amma suka yi ƙoƙarin kashe shi.
30
Sa’ad da ’yan’uwa suka sami labarin wannan, sai suka ɗauke shi zuwa Kaisariya suka aika da shi Tarshish.
31
Sa’an nan ikkilisiya ko’ina a Yahudiya, Galili da kuma Samariya ta sami salama. Ta yi ƙarfi; ta kuma ƙarfafa ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ta ƙaru sosai tana rayuwa cikin tsoron Ubangiji.
32
Da Bitrus yake zazzaga ƙasar, sai ya je ya ziyarci tsarkakan da suke a Lidda.
33
A can ya tarar da wani mutum mai suna Eniyas, shanyayye wanda yake kwance kan gado shekara takwas.
34
Sai Bitrus ya ce masa, “Eniyas, Yesu Kiristi ya warkar da kai. Tashi ka naɗe tabarmarka.” Nan da nan Eniyas ya tashi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options