Ayyukan Manzanni 18:1-11
1
Bayan haka, Bulus ya bar Atens ya tafi Korint.
2
A can ya sadu da wani mutumin Yahuda mai suna Akwila, ɗan garin Fontus, wanda ya je can ba da daɗewa ba daga Italiya tare da matarsa Firiskila, gama Kalaudiyus ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya tafi yă gan su,
3
da yake shi ma mai ɗinkin tenti ne kamar su, sai ya zauna ya yi aiki tare da su.
4
Kowace Asabbaci kuwa yakan yi muhawwara a majami’a, yana ƙoƙari yă rinjayi Yahudawa da Hellenawa.
5
Sa’ad da Sila da Timoti suka iso daga Makidoniya, sai Bulus ya ba da kansa ga yin wa’azi kaɗai, yana tabbatar wa Yahudawa cewa Yesu shi ne Kiristi.
6
Amma sa’ad da Yahudawa suka yi hamayya da Bulus suka kuma shiga zaginsa, sai ya karkaɗe tufafinsa a cikin rashin yarda, ya ce musu, “Alhakinku yana a kanku! Ba ni da wani laifi. Daga yanzu zan tafi wajen Al’ummai.”
7
Sai Bulus ya bar majami’ar ya kuma tafi ƙofar da take kusa da gidan Titus Yustus, mai yi wa Allah sujada.
8
Kirisbus, shugaban majami’a, da dukan iyalinsa suka gaskata Ubangiji; Korintiyawa masu yawa kuwa da suka ji shi suka gaskata, aka kuwa yi musu baftisma.
9
Wata rana da dad dare, Ubangiji ya yi magana da Bulus a cikin wahayi ya ce, “Kada ka ji tsoro; ka ci gaba da yin magana, kada ka yi shiru.
10
Gama ina tare da kai, ba kuma wanda zai fāɗa maka ya cuce ka, domin ina da mutane da yawa a wannan birni.”
11
Saboda haka Bulus ya zauna a nan har shekara ɗaya da rabi, yana koya musu maganar Allah.
Settings