2 Sama’ila 2:1-11
1
Bayan ’yan kwanaki, sai Dawuda ya nemi nufin Ubangiji ya ce, “In haura zuwa ɗaya daga cikin biranen Yahuda?” Ubangiji ya ce, “Haura.” Dawuda ya ce, “Wanne zan tafi?” Ubangiji ya ce, “Je Hebron.”
2
Saboda haka sai Dawuda ya tafi can tare da matansa biyu, Ahinowam daga Yezireyel da Abigiyel gwauruwar Nabal mutumin Karmel.
3
Dawuda kuma ya tafi tare da dukan mutanen da suke tare da shi, kowa da iyalinsa, suka zauna a Hebron da garuruwansa.
4
Sa’an nan mutanen Yahuda suka zo Hebron, a can kuwa suka naɗa Dawuda sarkin Yahuda. Sa’ad da aka gaya wa Dawuda cewa mutanen Yabesh Gileyad ne suka binne Shawulu,
5
sai ya aiki manzanni zuwa Yabesh Gileyad a ce musu, “Ubangiji yă albarkace ku saboda alherin da kuka nuna wa Shawulu ta wurin binne shi.
6
Bari Ubangiji yă nuna muku ƙaunarsa da amincinsa, ni kuma zan nuna muku irin wannan alherin saboda kun yi haka.
7
Yanzu fa, sai ku ƙarfafa, ku yi jaruntaka, gama Shawulu sarkinku ya mutu, gidan Yahuda kuwa sun naɗa ni sarki a kansu.”
8
Ana cikin haka, Abner ɗan Ner, komandan sojojin Shawulu, ya ɗauki Ish-Boshet ɗan Shawulu ya kawo shi Mahanayim.
9
Ya naɗa shi sarkin Gileyad, da na Ashuri, da na Yezireyel, da a kan Efraim, da Benyamin, da kuma na dukan Isra’ila.
10
Ish-Boshet ɗan Shawulu yana da shekaru arba’in sa’ad da ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi sarauta shekara biyu. Amma fa, gidan Yahuda, suka bi Dawuda.
11
Tsawon lokacin da Dawuda ya yi mulki a Hebron a kan gidan Yahuda, shekara bakwai ne da wata shida.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings