Skip to content
2 Sarakuna 14:8-14

2 Sarakuna 14:8-14

8
Sai Amaziya ya aika ’yan aika wurin Yehowash ɗan Yehoyahaz, ɗan Yehu, sarkin Isra’ila, yana tsokanarsa cewa, “Zo, mu sadu fuska da fuska.”
9
Amma Yehowash sarkin Isra’ila ya mai da martani wa Amaziya sarkin Yahuda ya ce, “Wata ’yar ƙaya a kurmin Lebanon ta aika da saƙo wurin itacen al’ul a Lebanon cewa, ‘Ka ba ɗana ’yarka aure.’ Amma wani naman jeji ya zo ya tattake ƙayar.
10
Tabbatacce ka ci Edom da yaƙi, yanzu kuwa kana ɗaga kai. To, ka gode da darajar da ka samu, amma ka zauna a gida! Don me kake neman faɗa kana neman fāɗuwarka da kuma ta Yahuda?”
11
Amma Amaziya bai saurara ba, saboda haka Yehowash sarkin Isra’ila ya kai masa hari. Shi da Amaziya sarkin Yahuda suka fuskanci juna a Bet-Shemesh.
12
Isra’ila suka fatattaki Yahuda, kowa kuwa ya tsere zuwa gidansa.
13
Yehowash sarkin Isra’ila ya kama Amaziya sarkin Yahuda, ɗan Yowash, ɗan Ahaziya, a Bet-Shemesh. Sa’an nan Yehowash ya tafi Urushalima ya rushe katangar Urushalima daga Ƙofar Efraim har zuwa Ƙofar Kusurwa, ratarta ta kai wajen ƙafa ɗari shida.
14
Ya kwashi ɗaukan zinariya da azurfa da duk kayan da aka samu a haikalin Ubangiji da kuma ma’ajin fadan. Ya kuma kwashi bayi sa’an nan ya koma Samariya.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options