2 Korintiyawa 8:9-15
9
Gama kun san alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi cewa ko da yake shi mawadaci ne, duk da haka, ya zama matalauci saboda ku, domin ta wurin talaucinsa, ku zama mawadata.
10
Ga shawarata a kan abin da ya fi muku kyau a wannan al’amari. Bara ku kuka fara bayarwa, kuka kuma zama na farko wajen niyyar yin haka.
11
Yanzu sai ku ƙarasa aikin da irin niyyar da kuka fara, ku yi haka gwargwadon ƙarfinku.
12
Gama in da niyyar bayarwa, za a karɓi bayarwa bisa ga abin da mutum yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.
13
Ba nufi nake yi a sawwaƙe wa waɗansu, ku kuwa a jibga muku nauyin ba. Amma ya yi kyau dai
14
a raba daidai wa daida, sai ku taimake su a yanzu da yalwarku saboda rashinsu. Wata rana su ma su taimake ku da yalwarsu saboda rashinku, don a daidaita al’amari,
15
kamar yadda yake a rubuce cewa, “Wanda ya tara da yawa, bai tara fiye da bukatarsa ba, wanda kuma ya tara kaɗan, bai kāsa masa ba.”
Settings