2 Tarihi 32:15-19
15
Yanzu fa, kada ku bar Hezekiya yă ruɗe ku yă kuma ɓad da ku haka. Kada ku gaskata shi, gama babu allahn wata ƙasa ko masarautar da ya taɓa iya ceton mutanensa daga hannuna ko kuwa hannun kakannina. Balle har Allahnku yă cece ku daga hannuna!”
16
Hafsoshin Sennakerib suka ci gaba da maganar banza wa Ubangiji Allah da kuma a kan bawansa Hezekiya.
17
Sarki ya kuma rubuta wasiƙu yana zagin Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana faɗin wannan a kansa, “Kamar yadda sauran allolin mutanen sauran ƙasashe ba su iya kuɓutar da mutane daga hannuna ba, haka Allahn Hezekiya ba zai kuɓutar da mutanensa daga hannuna ba.”
18
Sa’an nan suka yi magana da ƙarfi cikin Yahudanci wa mutanen Urushalima waɗanda suke kan katanga, don su firgita su, su kuma sa su ji tsoro don su iya cin birnin.
19
Suka yi magana game da Allah na Urushalima yadda suka yi game da allolin sauran mutanen duniya, aikin hannuwan mutane.
Settings